Kareem and Kareemat tare da Kakan su Maigirma Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau na muku barka da juma'a.
Mu soyayyar SHEKARAU gado ce a dangin mu, iyayen mu sunyi, mu muna yi, ya'yan mu zasu dora akai.
#JumaatMubarak #IbrahimShekarau #KareemAndKareemat
Kuyi scanning domin tattaunawa da SHEKARAU AI ta Whatsapp, manhajar da zata baku ingantattun bayanai akan Mallam Ibrahim Shekarau. Ka tambaye ta komai akan Sardaunan Kano zata amsa maka.
Naga wasu yan Kwaram suna babatun wai Abdussalam Abdulkarim Zaura yayiwa jam'iyyar APC wahala, da yayi mata me?
A'a Zaura ya fara Siyasar a shekarar 2019 inda ya tsaya takarar Gwamna a jam'iyyar GPN ya samu kuri'a 972 ko dubu daya bata kai ba.
Daga nan ya shigo jam'iyyar APC a shekarar 2021, inda Baba GANDUJE ya karbe shi da kuri'un sa guda 972.
Kafin duk wannan lokacin Maigirma Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau a shekarar 2013 ya narkar da jam'iyyar sa ANPP a matsayin sa na (Chairman, ANPP Merger Committee) ya shiga haɗakar APC da gwamnoni 3, sanatoci 7, majalisar wakilai 26, majalisar dokoki (can't remember), Ciyamoni ba adadi, da daruruwan kansiloli, millions of fans.
Naga wasu yara suna fadin ai Kwankwaso ne ya gina APC a Kano... February 2013 jam'iyyu suka hade officially, a watan June 2013 su Shekarau suka shigar jam'iyyar APC gaban INEC, a July 2013 INEC ta yiwa APC register. Duk an gama gwagwarmayar da tadiya, da tafiye tafiye da amsa tuhume tuhume, komai ya kammala duniya ta karbi APC, a watan November 2013 su Kwankwaso suka shigo. Shekarau yabar jam'iyyar i think February 2014.
Na dan tsallake wasu abubuwa a tarihin A'A ZAURA saboda dan jam'iyyar APC ne, abokin siyasar Maigirma Sardaunan Kano ne, muna mutunta shi, muna masa fatan alheri. Idan mabiyan sa suka cigaba da shigar mana hanci, tabbas zamu cire linzamin alkalamin mu.
Ita jam'iyya burin ta tayi nasara a duk zabuka... Saboda haka babu ta yadda tanaji tana gani zata bawa wanda bata da hope akansa takara ga wanda take ganin yafi alamun nasara.
Da Mal. Ibrahim Shekarau da A.A Zaura duk ta taba basu takara ta wannan kujerar Kano Central. Inda SHEKARAU ya kawo musu kujerar da rinjayen kuri'a mai nauyin gaske, shi kuwa A.A Zaura kifar musu da kujerar yayi da kuri'a mafi kaskanci a tarihin zaben Kano Central... A Kano Central ko an kada kai kana iya hada kuri'a 200+k amma akan A'A ZAURA aka fara samun kasa da wannan kuri'u, kayan yayi muni da yawa.
Tayaya kake tinanin jam'iyya tana ganin ga wanda yayi nasarar kawo mata kujerar da gagarumar nasara, zata tsallake shi ta bawa wanda ya shimfida ta da kasa wanwar dama. A siyasa fa kowa nasara yake nema, bafa tausayi ake ji ake bada takara ba. Naga wasu suna ta cewa yayiwa jam'iyya wahala ya kamata ta bashi dama, basu san shi tabawa damar zaben da ya wuce bane, akayi masa mummunan kaye? Wanda ke nuna alamar kujerar tayi masa girma ya nemi kasa da ita watakila zai iya nasara acan. Kuma a gayawa SHEKARAU wahaltawa APC, duk wanda yake cikin APC a yanzu albarkacin su Mallam Ibrahim Shekarau yake ci.
Muna girmama A'A ZAURA, muna masa fatan alheri, amma wannan gunagunin da rashin kunya da wasu daga cikin mabiyan sa suke yiwa Maigirma Sardaunan Kano, ba mafuta bace, kuma ina sa ran A'a Zaura zai taka musu birki don a hadu tare a tsira tare.
TSOKACI AKAN SABON SHIRIN LABARINA SEASON 15
An saki gajeren tallan (teaser) Labarina Season 15, wanda ya nuna cewa labarin ya shafi matsalar tsaro. Amma bisa nazari na akan tallan, na fahimci ba labari ne zalla akan rashin tsaro ba; labari ne akan soyayyar matasa guda biyu wadanda sanadiyyar garkuwa da mutane (kidnapping) suka hadu, da kuma sauran matsalolin da za su biyo bayan soyayyar tasu.
Wannan ya yi kama da salon da masu fim din DHURANDHAR na Bollywood suka yi; sun nuna tallan su kamar fina-finan ANIMAL ko MARCOS (masu nuna zallar zubar da jini), ashe sun boye asalin labarin ne sai wanda ya kalla zai gani. Ana zargin wannan na daya daga cikin sirrin nasarar fim din, domin mafi yawan fina-finan da suka bi wannan salon suna zuwa da labari mai gamsarwa. Ganin cewa kamfanin Saira Movies ne, tabbas muma muna sa ran ganin wani abu na daban.
DALILAI BIYAR DA ZASU SA MU KALLI LABARINA SEASON 15:
1. BANNER: Kamfanin Saira Movies ya yi fice wajen kawo fitattun fina-finai masu shauki da nuna kwarewa.
2. SEQUEL: Dorawa akan tsarin Labarina. Idan muka dubi sauyin da aka samu a labarin Sadiq Sani Sadiq, Amina Uba, da Fatima Hussain, muna sa ran wannan ma zai bada citta fiye da wancan.
3. SABON DARAKTA: Karo na farko da Darakta Aminu Saira ya bar kujerar bayarda umarni ya mikawa Ali Gumzak, wanda babban darakta ne da ya yi fina-finai ingantattu a kwanan nan kamar Manyan Mata, Jini Daya da Jamilun Jidda. Muna dokon ganin irin sabon salon da zai kawo.
4. NEW PAIR: Hadin jarumi Abubakar Sadiq Umar (Zaka) da Asiya Aliyu Auta ya zo a daidai lokacin da masu kallo suke kishirwar sabbin fuskoki masu hazaka.
5. INGANCIN DAUKAR HOTO: Tallan shirin ya nuna wani babban mataki na kwarewa a fannin hoto (cinematography and VFX) wanda ba a saba gani ba a Kannywood.
Shirin zai fara zuwar muku gobe Juma'a a tashar Saira Movies TV (YouTube 8:30pm - Satellite 9:00pm).
Ku me kuka fi dakon gani a cikin wannan fim din? Ku fada mana a comment section.
#LabarinaSeason15
#SairaMovies
#LabarinaSeries
#LabarinaRanarJumaa
#Kannywood
Zanyi wani rubutu akan sabon LABARINA SEASON 15, canjin salo, trailer cut din, jaruman shirin da kuma Director din.
Kafin nan, kuje ku sake kallon Trailer din da wakar da filmmakers din suka saki zuwa iyanzu, don muyi tattaunawar ilmi akai, idan na futar da rubutun zuwa gobe Insha Allah.
#LabarinaSeason15
#SairaMovies
#LabarinaSeries
#LabarinaRanarJumaa
#Kannywood
Ruwan Dare Series Trailer Review
By Usman Solo
I recently caught the trailer for the Ruwan Dare series, which serves as a highly anticipated sequel to the 2018 blockbuster movie of the same name.
For those who championed the original film, this series is bound to be a thrilling successor. Leading men Aminu Shariff Momo and Sadiq Sani Sadiq return to the screen, delivering a masterclass in acting. They flawlessly portray the arrogance and intellectual vanity often seen in graduates who believe their degrees entitle them to everything—all woven into a rich tapestry of sharp, witty comedy.
The trailer is a vibrant promise of unfiltered humor and a poignant satire on the elitist mindset of some educated elites. This time, the production has bolstered its ranks with a stellar supporting cast that adds immense depth and flair to the footage.
I am fully convinced this series will be a captivating sensation for the audience. A massive salute to the visionary Producer and Director, #YaseenAuwal, for his creative direction.
The official trailer will be unleashed in less than 30 minutes on the @sairamoviestv and Yaseen Auwal YouTube channel.
BREAKING NEWS: AN KADDAMAR DA SHAFIN YANAR GIZO NA SARDAUNAN KANO, MALLAM IBRAHIM SHEKARAU – NA FARKO MAI AMFANI DA AI! 🌐✨
Muna farin cikin sanar da al'umma cewa an buɗe sahihin shafin yanar gizo na tsohon Gwamnan Jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano). Wannan shafi ba kawai wurin karanta labarai ba ne, rumbun tarihi ne da fasaha na zamani.
Abubuwan da za ku samu a shafin:
✅ Tarihi da Ayyukan Alheri: Cikakken bayanin rayuwar Malam Ibrahim Shekarau tun daga haihuwa, aikin gwamnati, har zuwa matsayinsa na yanzu a jam'iyyar APC.
✅ Rumbun Tarihi (Archives): Akwai ɓangare na musamman da ke ɗauke da tsoffin labarai da hotuna na tarihi waɗanda ba za ka same su a ko'ina ba sai a wannan shafin.
✅ Fasahar AI (Na farko a Najeriya): Muna Alfaharin sanar da ku cewa ana saka na’urar Artificial Intelligence (AI) a shafin. Wannan shi ne karon farko da wani ɗan siyasa a Najeriya ya samar da wannan fasaha don amsa tambayoyi da taimaka wa masu ziyara.
✅ Tambayoyi da Amsoshi (Q&A): Akwai ɓangaren da za ka iya samun amsoshin tambayoyin da suka shafi manufofinsa da ayyukansa.
✅ Hotuna da Bidiyo: Kayatattun hotuna da bidiyoyi masu inganci (HD) na ayyukan jin daɗin jama'a da Malam ya gudanar.
Wannan babban mataki ne na amfani da fasahar zamani wajen adana tarihi da kuma kyautata sadarwa tsakanin shugaba da al'umma.
Ziyarci shafin yanzu:
🔗 [ / ]
#Shekarau #SardaunanKano #AIinPolitics #KanoState #APC #Nigeria #Innovation #Leadership
Why is Abdul M. Sharif such an underrated actor in Kannywood?
Na jima ina kallon jarumi Abdul M. Shareef a matsayin daya daga cikin hazakan jaruman da masana’antar Kannywood take kokarin wofantarwa. Idan aka duba dukkan abubuwan da ake bukata ga babban jarumi (Complete Actor), Abdul ya hada su; yana da kwarjini da siffa (physique), yana da kwarewa (skills), kuma fuskarsa tana fitar da ma’anar da ake bukata a kowane yanayi (expression).
Baya ga iya rawa, Abdul na iya fitowa a kowane matsayi ko na dan birni mai wayewa ko na bakauyen da bai san komai ba. Tsawon sa da kwarjinin sa na ba shi damar dacewa da kowace irin jaruma. Sannan yanayin muryarsa (flexible voice) yana ba shi damar juyawa tsakanin kalaman soyayya masu sanyaya zuciya, ko kuma muryar barazana a lokacin fada da tashin hankali. Kai, har ma a fannin barkwanci (comedy), Abdul ya nuna zai iya taka rawar gani.
Abin tambaya a nan shi ne: Me ya sa masana’antar Kannywood ba ta mararin jarumin? Bayan kallon fim din Mujadala na kamfanin FKD, na zata furodusoshi za su fara rubibin sa a manyan ayyukansu, amma sai aka sake komawa gidan jiya. Fina-finai irin su Mujadala, Jani Muje, da Yaki A Soyayya, sun tabbatar da cewa Abdul jarumi ne da kowace masana'antar fina-finai za ta yi alfahari da shi.
Na sani cewa bayan kwarewa, akwai sauran abubuwan da suke sa jarumi ya zama gwanin furodusoshi (Darling Of Filmmakers), musamman kyakkyawar mu’amala da daukar aiki da mahimmanci (professionalism). Masu shirya fina-finai ba sa son jarumin da zai janyo musu asara ta hanyar kin zuwa wurin aiki akan lokaci, ko kawo tsaiko lokacin da aka kusa kammalawa, ko kuma janyo cece-kuce da zai shafi mutuncin fim din. Idan jarumi yana da irin wannan dabi’u, to duk iyawarsa, jingine shi ake yi, kamar yadda aka yi wa jaruma Kangana Ranaut a Bollywood.
Shin ko Abdul M. Shareef ma yana da irin wadannan dabi'u ne da suka zama masa tarnaki? Mutanen cikin masana'antar ne kawai za su iya bada wannan shaidar.
A matsayina na masoyinsa (fan), na rubuta wannan ne domin koka yadda tafiyar aikinsa (career) take, domin a nawa gani, kwarewar da yake da ita ta kai ya zama daya daga cikin wadanda suka fi kowa tashe (reigning superstar) a halin yanzu.