Home bbchausaPosts

BBC News Hausa

@bbchausa

Hotuna da bidiyo masu jan hankali da suka shafi rayuwarku
Followers
2.8m
Following
43
Account Insight
Score
76.88%
Index
Health Rate
%
Users Ratio
66170:1
Weeks posts
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da na Amurka Donald Trump sun bayyana farin cikinsu bayan sojojin ƙasashen biyu sun kashe jigo a ƙungiyar ISIS a duniya, Al-Mainuki. Ga cikakken bayani kan dan ta'addan wanda ya yi fice wajen tara wa ƙungiyar kuɗaɗe da ɗaukar mayaƙa. 🎥 - Fatawul Mohammed/Abba Auwalu
710 21
3 hours ago
Antoine Semenyo ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Man City nasara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Wannan ne kofi na biyu da ƙungiyar ta lashe a kakar wasa ta bana bayan lashe kofin Carabao a baya-bayan nan. Kuna ganin City za ta iya lashe kofi na uku a bana?
1,655 21
5 hours ago
Barcelona ta sanar cewa Robert Lewandowski zai bar ƙungiyar bayan ƙarewar kwantiraginsa a ƙarshen kakar wasa ta bana. Ɗan wasan na Poland ya koma Barca ne a 2022 inda ya zura ƙwallo 119 zuwa yanzu tare da lashe kofuna bakwai. Yaya za ku kwatanta rawar da ya taka a Barca?
2,481 38
9 hours ago
Cikin wata wasiƙar janyewar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abin Al-ajabin Zazzau ya sanar da janye takarar tasa ne nan take. Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da jagororin jam'iyyar APC da kuma iyalai da abokan arziki. Sai dai bayan tantancewar an fara taƙaddama kan shekarunsa musamman a shafukan sada zumunta, inda ake zargin ya yi aringizon shekaru, saɓanin yadda yake bayyanawa.
7,259 277
10 hours ago
A wani sako da ya walllafa a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka, ya ce, Abu-Bilal al-Minuki - wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a ISIS - na ɓuya ne a Afirka. Trump ya bayyana al-Minuki - a matsayin ɗan ta’adda lamba ɗaya, da mafi tasiri a duniya, kuma ya ce kawar da shi da aka yi, ayyukan ƙungiyar ISIS, na duniya za su ragu matuƙa. Shugaban na Amurka ya kuma gode wa gwamnatin ta Najeriya kan haɗin gwiwar da suka yi wajen wannan aiki, sai dai bai bayar da wani ƙarin bayani ba baya ga haka ba.
4,529 156
12 hours ago
Birnin Kano ya sake samun tagomashi yayin da Abdul Samad Rabiu ya zama mutum na biyu mafi arziƙi a Afirka, wato yanzu attajirai biyu mafi tarin dukiya a nahiyar duk Kanawa ne. Ga bayanin yadda kuɗin BUA ke ƙaruwa babu kaƙƙautawa. 🎥 - Abba Auwalu
3,894 56
17 hours ago
Ga wata arangama! Kalli yadda wasu karkanda guda biyu suka yi faɗa a bakin wata kasuwa da ke ƙasar Nepal.
727 7
1 day ago
Kamfanin ƙera motoci, Honda ya tafka asara karon farko a shekara cikin shekaru 70 saboda hannun jarinsa na motoci masu amfani da lantarki ba su haifar da riba ba. Ba a cika neman motoci masu amfani da lantarki ba kamar yadda kamfanin ya yi hasashe inda kamfanin na Honda ya ce ya yi asarar dala biliyan 2.68 zuwa Maris ɗin 2026. Kamfanin ya ce zai soke wasu daga cikin muradansa na samar da motocin lantarki kuma zai nemi wasu kayan aiki daga China inda farashinsu suka fi sauƙi. Kamfanin ya ce tsare-tsaren Amurka suna da hannu wajen asarar da ya tafka ciki har da ƙaƙaba haraji.
5,567 44
1 day ago
Teloli da dama a wannan shekarar sun yi amannar cewa an fi kawo musu ɗinki a lokacin sallar layya. Sai dai wasu na ganin kamar an fi caɓa ado a sallar azumi duba da rashin hidindimu irinsu yanka da kuma gyaran nama.
2,660 102
1 day ago
Kun taɓa ganin kasada irin wannan? Wannan dattijuwar ta hau fuffuken jirgin sama yayin da yake tafiya don murnar cika shekaru 80 a duniya.
734 21
2 days ago
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban Najeriya a zaɓen shekarar 2027, inda ya ce zai nemi kujerar ne ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM). Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani babban gangamin haɗakar jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a Ibadan. Sanarwar ta Makinde ta ja hankalin dubban magoya baya da masu ruwa da tsaki da kuma abokan siyasarsa, lamarin da masana ke gani a matsayin wani muhimmin mataki a sauye-sauyen siyasa da ke ci gaba da faruwa gabanin babban zaɓen gaba.
2,873 32
2 days ago
Ko kun har yanzu akwai sirrukan sararin samaniya masu yawa da ba a sani ba? Wata naʼurar hangen duniyoyi ta gano wasu gungun duniyoyi da taurari karon farko a tarihi.
6,242 176
2 days ago